Minggu, 1 November 2026

DVP Berita

Terkini
Houthi

Saudi Arebiya ta kakkabo makaman Houthi a birnin Riyadh

Dakarun sun lalata jirage marasa matuka da makamai masu linzami a Riyadh da tekun Baharmaliya da kuma yankin Yanbu mai tarin bututan man Saudi Arebiya.

Sumber foto: DW.com

Dakarun kawancen tsaro da Saudi Arebiya ke jagoranta, sun samu nasarar dakile hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuka da 'yan 'yan tawayen Houthi na Yemen, suka harbawa birnin Riyadh a wannan Juma'a da ma wasu yankunan kasar.

Karin bayani:MDD ta yi tur da hare-haren da 'yan tawayen Houthi na Yemen ke kai wa Saudi Arebiya

Sanarwar da kakakin rundunar hadin gwiwar, Turki al-Malki, ya wallafa a shafinsa na X, ta ce jirage uku marasa suka kakkabo a kudancin birnin Riyadh, sai wasu makamai biyu masu linzami a tekun Baharmaliya.

Karin bayani:'Yan tawayen Houthi na Yemen sun kai hari kan fadar gwamnati a Aden, yayin da kawancen sojan Saudiyya ya yi bayani kan hare-haren da aka kai kasar.

Haka zalika sun lalata wasu makamai masu linzami a yankin Yanbu, na gabar Baharmaliya, mai tarin bututan man Saudi Arebiya.

Sumber: DW.com. Baca selengkapnya di sumber

Artikel terkait

Berita terbaru

Tinggalkan komentar

Alamat email Anda tidak akan dipublikasikan. Ruas yang wajib ditandai *

Share with