Minggu, 1 November 2026

DVP Berita

Terkini
Houthi

Hadarin jirgin sama a Saudi Arebiya ya janyo asarar rayuka

Garkuwar tsaro samaniyar Saudi Arebiya ta kakkabo makamai masu linzami da jirage marasa matuka na 'yan tawayen Houthi.

Sumber foto: DW.com

Rundunar kawancen tsaro da Saudi Arebiya ke jagoranta, ta tabbatar da mutuwar mutane biyu, sanadiyyar hadarin jirgi mai saukar ungulu a yankin Najran na kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar Turki al-Maliki ya fitar a yau Lahadi, ta ce jirgin ya fadi ne a kusa da ma'aikatar kula da tsaron cikin gida.

Karin bayani: Dakarun kawancen tsaro da Saudi Arebiya ke jagoranta sun dakile hare-haren Houthi a Riyadh

To sai dai kungiyar 'yan tawayen Houthi na Yemen, mai samun goyon bayan Iran, ta yi ikirarin cewa ita ce ta harbo jirgin, bayan da ta gano shirinsa na kai ma ta hari, kamar yadda mai magana da yawunta Yahya Saree ya sanar a shafinsa na X.

Lardin Najran na kudu maso yammacin Saudi Arebiya, na cikin yankunan da ke fama da hare-haren 'yan tawayen Houthi na Yemen a 'yan makonnin nan, sakamakon fadadar rikicin bangarorin biyu.

Karin bayani:MDD ta yi tur da hare-haren da 'yan tawayen Houthi na Yemen ke kai wa Saudi Arebiya

A gefe gu garkuwar tsaro ta sararin samaniyar Saudi Arebiya ta samu nasarar kakkabo makamai masu linzami da jirage marasa matuka na kungiyar 'yan tawayen Houthi a wasu sassan kasar.

Wannan na cikin sanarwar da kakakin rundunar kawancen tsaro da kasar ke jagoranta Turki al-Maliki ya fitar a wannan Lahadi, ba tare da bayyana irin barnar da hare-haren suka yi a Saudiyyar ba.

Karin bayani: Iran ta yi tayin sasanta Saudiyya da 'yan Houthi

Sanarwar ta ce dakarun sun lalata makamai masu linzami da jirage marasa matuka biyu a kusa da birnin Riyadh.

Sai jirgi marar matuki da shi ma suka harbo a gabashin kasar.

Sumber: DW.com. Baca selengkapnya di sumber

Artikel terkait

Berita terbaru

Tinggalkan komentar

Alamat email Anda tidak akan dipublikasikan. Ruas yang wajib ditandai *

Share with